Kalaman soyayya
❤ ZUWA ❤ GA ❤ MASOYA ❤
❤❤ ARMASHIN SOYAYYA ❤❤
❤❤ Soyayya tana da wadansu 'yan tanade tanade da akeyimata domin kara samun armashi da tasiri a zukatan Masoya ❤❤
❤❤ Mafi akasarin masoya suna dauka cewa da zarar kun amincewa juna, to shikenan ba sauran soyayya, alhalin kuwa abin ba haka yakeba domin da zarar kun amincewa junanku to alokacin ma aiki yake mai girma domin ita soyayya tamkar wata sabuwar shuka ce dole sai ana bata ruwa ana zuba mata taki da kuma gyara sannan tayi armashi har takai ga ta inganta, matakan kuwa sunhada da ❤❤
🌺🌺 1 Fadin gaskiya a dukkannin kalamanka duk da cewa wadansu 'yan matan sunfi son samari 'yan karya amma dai fadin gaskiya a cikin sha'a nin soyayya yakan kara sawa ita yarinyar ta ringa gasgata duk abin da ka fada mata sannan kuma ta ringa yimaka biyayya a cikin soyayyarku Lima bazata ringa shakka ko zarginka ba 🌺🌺
🌺🌺 2 Tausayi idan har yakasance kana tausayawa masoyinka tabbas shima zai ringa tausaya maka hakan zai kara karfafa kashin bayan soyayyarku, kuma hakan na haifar da kyakkaywar mu'amala da zaman takewa mai dadi 🌺🌺
🌺🌺 3 Kyautatawa anan kyautatawa yana nufin bayar da wani Dan tukuici akan siyayyar da ake yimaka, kyauta ko yaya take batayin kadan ga masoyi 🌺🌺
❤❤ Ba lallai sai ka dauki kudi kabawa masoyinkane, kadai zaka nuna cewa ka kyautata masa, A, A akwai abubuwa da sukan kara armashin soyayya idan anbaiwa masoyinsu ❤❤
🌸🌸 1 ZOBE. Idan har kabawa masoyiyarka ki ka bawa masoyinki kyautar ZOBE. To zaya kara armashin soyayyar , saboda aduk lokacin da ya kalli wannan ZOBEN.dake sanye a Dan yatsanshi zai tunu da masiyinnan nasa 🌸🌸
🌸🌸 2 HOTO. Shima yana taka muhimmiyar rawa gurin ganin soyayya ta kara yin armashi domin idan har ka dauki HOTON ka ka baiwa masoyinka to tabbas wannan masiyin naka zai yi maka masauki na musamman a cikin zuciyarsa domin duk lokacin da ya kalli wannan HOTON to zai kara jin kaunarka a cikin zuciyarsa 🌸🌸
🌸🌸 3 TURARE. kyautar turate tana kara armashin soyayya domin duk lokacin da aka baiwa masoyiyarka kyauta turate zata kara jin kaunarka ya shiga cikin zuciyarta, domin duk lokacin da ta fesa wannan turaren kamshinsa ya dokar mata hanci to bawanda zata fara tunawa sai kai 🌸🌸
🌸🌸 4 FULAWA. Kyautar fulawa ko fure shima yana kara taimakawa armashin soyayya kwarai da gaske 🌸🌸
🌸🌸 5 KATI. Kyautar kati mai dauke da kalaman soyayya shima yana kara armashin soyayya kwarai da gaske 🌸🌸
🌷🌷 🌷🌷
🌷🌷🌷🌷
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤😀✋
Da kyau
ReplyDelete