Maza da mata

_*🌹  ♡KALAMAN SOYAYYA♡   🌹*_
                             
           _*💜ABINCIN ZUCIYA💜*_

       _*↓DARASINMU NA YAU SHINE↓*_

_*🎶LAFUZAN SO A🎶*_

_*🌃✨RANAKUN BIKIN SALLA.✨🌃*_

_*🧡SARAUNIYAR BIRNIN MASOYA.❤*_

_🌹A duk lokacin da na zauna ina yin nazari a dangane dasu soyayyar mu, sai na hasaso cewa dama a ce fikafikai za  bayyana a jikina da na nausa da ke izuwa kayatacciyar fadar dake canyan babban birnin masoya na sabuwar duniyar mu domin sada ki da kujerar alfarma ta mukamin sarauniyar ‘ matan duniya da na dade da baki. Shin Rukayya kin kuwa lura da cewa ina neman na zamaiya zautacce a cikin soyayyar ki? Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan  fita ba. Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki. Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta. Fatana dai mafarkina ya zamo gaskiya a dangane da ke._
BARKA DA SALLAH.

_*💙ZAN ZAMO MIKI GARKUWA.🧡*_

🌹Alkawari ne naa dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matukar muna  tare da juna, ina fatan nan da wani dan lokaci ki tabbatar da hakan bayan kin zamo mata a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Fatima, ki huta lafiya. Ki kula min da kanki. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH._

_*💚KINA DA KYAU MASOYIYATA.💜*_

🌹Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske? Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni d’aya cikin kad’aici a dare ko safiya. Ke ce abar so na.
BARKA DA SALLAH._

_*💙ZAN BAYYANA MAKA SIRRINA.💛*_

🌹Amincin Allah ya tabbata a gare ka sahibina, a yau ne nake son na kara bayyana maka matsayin ka a gare ni, tabbas Abba ka zamo wani jigo na dorewar farin ciki a zuciyata. Fuskar ka ce abun da nake kallo na samu farin ciki cikin gaggawa. Karda ka damu ‘Dan-Hausa da rashin bayyana maka gaskiyar al’amari amma a yau ranar sallah kuma ranar farin ciki da murna nake son furta maka cewa ina son ka! Ina son ka!! Ina son ka Abba!!! Daga masoyiyarka Rukayya.
BARKA DA SALLAH._

_*💚DAMA A CE HAKAN YA KASANCE A ZAHIRI.❤*_

_🌹A kullum na kan yi mafarkin ga mu a tare cikin d’aki tare da ‘ya’yan mu, shin ko hakan yana nufin za mu mallaki juna kenan? Tabbas idan hakan ya kasance bani da wani sauran buri a rayuwata face na yi fatan kasancewa a tare da kai a gidan aljanna. Ina son ka, ka kula min da kanka karda ka bari kowace kazamar yarinya ta rabe ka. Ni ce taka Mardiya.

Comments

  1. https://mynovels.com.ng/gidan-uncle/

    https://mynovels.com.ng/kalaman-soyayya-masu-dadi/

    ReplyDelete
  2. Thank You and that i have a swell provide: Where To Start House Remodeling remodel outside of house

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Rumbun kalamai

Kalaman Soyayya queen Fatima Zahra