Rayuwace
RAYUWA MAI IYAKA
✒ Jiya wasu sun tafi
✒ Yau wasu za su tafi
✒ Gobe ma za'a raka wasu qabari
✒ Abin fata ga kowa karshe mai kyau
✒ Haka kuma dafatan samun ni'ima
✒ Da rayuwa mai dadi cikin qabari
✒ Kuma na tabbata kowa na burin samun Hisabi
mai sauki
✒ Da shiga Aljannah
✒ Abin tambaya da dubawa anan muna yiwa
kanmu tanadin hakan?
Indai ni da kai da ke duk bamu san ranar tafiyar
mu ba,
To,
Meyasa bama kokarin zama cikin shiri ta hanyar
tsoron Allah da kiyaye umurni da hani da dagewa
wajen bin Sunnah
Da neman yardar Allah?
✒ Mu sani tare da mu akwai masu rubuta
ayyukanmu da furucinmu...
✒ Lallai mutuwa tilas ce akan kowa, yadda ake
kai wasu qabari da kai, kaima haka wasu zasu
kaika.
✒ Yadda muke jimami da damuwar rabuwa da
makusanci,
Haka dangi da masoya zasu rabu damu
watarana.
✒ Qabari wuri ne masaukin farko ana tambayoyi
a cikinsa kuma ana fara gamuwa da ni'ima a
cikinsa
✒ Wasu kuma daganan za su fara dan-danan
azaba acikin kunci da matsi, Allah ya tsaremu
"Yan uwa don Allah muyiwa kanmu tanadi, muji
tsoron Allah
Mu kiyaye hakkin junanmu, mu tsare amana ta
al'umma da ta iyalanmu da duk wanda alakar
zaman tare ya hadamu.
Mu kame harshenmu akan aibata juna, ka da
muyiwa juna hassadako mugunta.
Mu bude zukatanmu wajen sulhu da yafewa indai
an 6ata mana.
Mu saukaka cikin Magana da Hulda da
Rangwame.
Muji tausayin junta....
Allah yasa mudace
Na tabbata babu Wanda keyiwa kansa fatan
tsanani,
Don haka mu kiyaye cikin ayyukanmu don samun
saukin rayuwa mai dadi.
ALLAH YA GANAR DAMU YABAMU IKON AIKATA
ALHERI AMEEEN.
Comments
Post a Comment