11

[8/18, 7:38 AM] +234 806 165 4148: *ILLAR FUSHI*

Fushi  tamkar tabin hankali ne Karshen shi kuma Nadama ne, Inji *Aliyu Bin AbiTalib (R.A)* Ka lura Duk wanda *fushi* ya shafe shi yakan fidda shi daga dabi'a irin ta mutane *,FUSHI* shine tarkon abin da shaidan yafi amfani da ita wajen halaka dan adam. Inji Ibnul Qayyim.Ka lura in mutum yana cikin *fushi* to yakan iya aikata komai... a fusace Sannan Ba'a gane mutum me hakuri sai a lokacin *FUSHI* . Maganin fushi  *manzan Allah* (s a w) yace idan kai *fushi* idan kana tsaye ne *kazauna* idan kana zaune ne *ka kwanta* ko kuma *kabar wurin* da aka saka kai fushin. *Ya Allah* kasa mu iya hadiye *fushin* mu, mu iya yafe ma "yan uwan mu dan mutsira ranar gobe kiyama. *ALLAH*  ka jikan iyayenmu da yanuwanmu,da abokan mu, *Ya ALLAH* ka sa mu gama da duniya lfy.
*BARKA DA WARHAKA*
[8/18, 12:11 PM] +234 806 880 6706: *Muyi Aiki Tare Da Lura👂🏻👈🏻*
Kai Bawan Allah menene kuma na yin wani bikin birthday wai don ka cika shekaru hamsin a duniya?

Shekaru hamsin fa da yawa, domin ko taku ka keyi daya-daya da kafar ka na tsahon shekaru hamsin idan ka waiwaya bayan ka zaka ga ashe kayi nisan zango.

A maimakon wannan birthday din da za kayi mara anfani ai gwara kayi nadama iri biyu:
*ta daya:* tsahon shekaru hamsin din da kayi, shin wadan ne irin aiyuka na alkhairi ka keyi? Domin ka kara a kan su, saboda baka da tabbacin zaka kara yin wasu shekaru hamsin din a duniya.

*ta biyu:* tsahon shekaru hamsin din da kayi, shin wadan ne irin aiyuka na sharri ka keyi? Domin ka tuba ka dena su, saboda baka da tabbacin zaka kara yin wasu shekaru hamsin din a duniya.

Yaa Allah Kasa muyi kyakyawan karshe🤲🏻

Domin cigaba da samun irin wadan nan fadakarwa tamu ku biyo mu a wannan number 👉🏻08068806706.
*'Dan Uwan Ku Musa Ali Tahir (Gaza)*
[8/18, 12:11 PM] +234 806 880 6706: *Muyi Aiki Tare Da Lura👂🏻👈🏻*
Kai Bawan Allah menene kuma na yin girman kai idan ka tuno asalin ka?

*Na daya:* an halicce kane saga ruwan maniyyi wanda baifi cikin cokali daya ko biyu ba.

*Na biyu:* sai aka mayar da kai gudan jini wanda baifi cikin kofi daya ba.

*Na uku:* sai aka mayar da kai gudan tsoka wacce ba tafi mutum daya ya cinye ta ba.

*Na hudu:* sai aka sanya maka kasusuwa kuma aka busa maka rai.

*Na biyar:* annan kazo wannan duniyar ta kofa me rauni inda fitsari yake fitowa.

Kuma duk kwarewar likitotin duniya basu isa su canza wannan asalin naka ba.

Kai bawan Allah tuno wannan asalin naka kadai ya isa ka daina girman kai da dagawa a bankasa.

Yaa Allah Kasa muyi kyakyawan karshe🤲🏻

Domin cigaba da samun irin wadan nan fadakarwa tamu ku biyo mu a wannan number 👉🏻08068806706.
*'Dan Uwan Ku Musa Ali Tahir (Gaza)*
[8/18, 12:11 PM] +234 806 880 6706: *Muyi Aiki Tare Da Lura👂🏻👈🏻*
Kai Bawan Allah menene kuma na yawaita dogon buri idan ka tuno karshen ka?

Lalle wata rana zaka zama gawa kuma da ace za a nuna maka wannan gawar taka da sai ka rena kan ka da kan ka kuma duk irin son da masoyan ka suke yi maka baza suce a bar musu gawar ka ba suna so domin a wannan lokacin ka zame musu abun tsoro.

Kash! Amman duk da haka kana tara kudin baza ka dauwama kana cin su ba, kana gina gidajen da baza ka dauwama a cikin su, kana siyan motocin da baza ka dauwama kana hawan su ba, kana siyan suturar da baza ka dauwama kana saka su ba.

To ka sani cewa dayan abu biyu zai iya faruwa cikin dukiyar da ka tara kaqi ci kuma kaqi ciyarwa! Kodai ciwo ya same ka su kare a wajen neman magani! Ko kuma ka mutu ka barwa magada suyi abun da suka so da ita.

Yaa Allah Kasa muyi kyakyawan karshe🤲🏻

Domin cigaba da samun irin wadan nan fadakarwa tamu ku biyo mu a wannan number 👉🏻08068806706.
*'Dan Uwan Ku Musa Ali Tahir (Gaza)*

Comments

Popular posts from this blog

Rumbun kalamai

Maza da mata

Kalaman Soyayya queen Fatima Zahra